Chapter 14 Reading Rahima Complete Hausa Novel.txt (2025)

hakan na ganta ko gaisawa ba muyi ba."

Yace "Mutumiyar banza kina nufin kin kwaso kafafunki ne kinzo muyi miki mene, mu hana sa aure? Wallahi Mamana (haka yake kiranta saboda sunan mahaifiyarsa yasa mata) kin ban kunya, ban taba tunanin ba zaki zauna gidan aureki cikin mutunci ba,yarinya kin zama sai kace goyon arna?"

Hjy Lami tace "Ya za ayi mijinki ya kalleki da mutunci bayan kin zama tamkar maras mafadi?"

Ta saka kuka "Wallahi Mama Haseeb kazafi yake mini."

Alh Muhd ya sake daka mata tsawa "Rufa min baki ko in tashi in tattakaki, wallahi muddin baki canza dabi''unki ba daga yau mun sa kafar wando daya ni dake, bar ganin na sake miki ina ksunarki, zata koma kiyayya tsakaninmu Kuma kin sanni sarai kamar yunwar cikinki, wallahi ko ke kadai na haifa ina iya yafeki har abada don banga amfaninki ba."

Hjy Lami ta kalleta cikin bacin rai tace "Dubeki yarinyarki dake kin bata rayuwarki da kanki ga kinan duk kin jeme kin lalace, Kuma da kike cewa kazafi likitan ke miki su mutanen duniya da kike mu'amala da kawayen banzan da kike hulda dasu duk kazafin ne? Duk inda kika shiga ana ga 'yar wance da wane."

Alh Muhd yace "Dalili kenan da muka bashi goyon bayan ya auro mai mutunci tunda ke kin zubar da naki, idan kinga ba Zaki iya zama dashi ba ga hanya nan bude to banga amfanin zama da igigiyar aurensa a kanki ba, sai kije kiji da zunubi daya."

Uwar ta fashe sa kuka "Alhaji kalli yarinyar nan ka gani ba abinda ta sawa gaba sai burin duniya da kyale-kyale, dan rayuwar da take takaitatta. Wai don Allah wane irin gata ne ba a nuna miki ba? Me kika nema kika rasa a gidanku ko na mijinki? Allah ya hore dukiyar da ake taimakawa wasu ma, to me kike nema ne?"

Maimakon ta nuna alamun nadama sai ta dauko wani zancen da bai danganci fadar da ake Mata "Mama ni gaskiya ba Zan zauna da kishiya ba, kishiyar ma yarinyar data san sirrina, bayan duk wata takama da Haseeb ke yi da wani ji da kai, mahaifina ne silar duk abinda ya samu, duk abinda yake takama dashi Kai dinnan Baba kaine sanadin, ko yana nufin anci moriyar ganga ne za a yarda kaurenta, to gaskiya Baba da sake...

Bata ga mikewarsa ba, ji tayi kawai an dauketa da tafi ta kifa kasa, ya bita ya taka yana zagi, uwar ma ta rufeta da duka, Nan ta fara kwarma ihu sauran matan gidan suka taru don cetonta..
Da kyar da rarrashi aka kwaceta, ko kafin ayi haka fuska ta kumbura jiki ya murzu da duka.

Alh Muhd ya fara haki, jiri ya kwashe shi, matan suka tareshi, akayi hanzarin dauko masa maganin hawan jininsa aka bashi yasha kana suka kamashi ya koma daki ya kwanta.

Hjy Lami ta dawo dakinta ta cimma 'yar nata kuka tace "Ya jikin Baban?"
Ta kalleta ta watsar "Tashi ki bace min da gani, ina ruwanki da jikinsa? Ai kinsan yanada hawan jinin don kece sanadi, to ki dage ki zama kece ajalinsa."
Ta Kara fashewa da kuka "Don Allah Mama ku yafe min, Allah zan daina komi, bacin raine yasa Ni fadin wannan maganar."
"Da gangar kika yi tunda an Sha gargadinki kan furucin da kike yi, yau kika yiwa mijinki gorin? Maras tunani, da kike fadin ubanki ne silar arzikinsa yanzun hidimar da yake mana ya zama ke Kika sa shi? Yarone dan halas da yasan darajar iyayensa da naki."

Ta daga kai "To Ni Mama so kuke in zura masa ido Kan batun aurensa?"

"Ah ah kike kiyi abinda zaki iya kinji zabin da muka baki ai. Ni tashi ki fita min a daki, ki Kuma dauki yaranki ki maida gidan ubansu tunda baki San ciwon kanki ba, albasa bata yi halin ruwa ba."
10/09/2020, 18:03 - Anty saliha: ....RAHIMA...doc by jami

25
Zuwaira ta tabbatar wa kanta ba zata sami yadda take so wajen iyayenta ba, saita canza shawara ta tuntubi Husaina daya daga cikin kawayenta a tunaninta ita din ce kadai zata iya taimaka mata warware matsalarta.
Tafiya mikakkiya ta isa gidan Husaina dake gadon albasa, Sha daya saura na safe ta matsa kararrawa, saurayin dake mata wanki da guga ne ya bude mata kofar ta shiga yana gaisheta ta tambayesa "Ina Hajiyar?'

"Tana ciki." Ya amsa.
Kai tsaye ta wuce bedroom din Husaina ta taras da ita a kwance "Lalle kina jin dadinki, ni ina ga time din barcin safe?"

Tayi Mika tace "Zuwaira Wai Ina kika shigane tun safe nike neman wayarki?"
Zuwaira ta zauna bakin gado "Kinga ni yunwa nike ji bari in ci abinci tukunna kisha newa."

Husaina ta dago ta kalli yanayin fuskarta ta saka salati ,"Ke ya aka yi haka?"

Tace "Labarine mai tsawo bari in koshi jikina har rawa yake, rabona da abinci tun jiya wajen bukin nan."

Cikin hanzari ta kira yaron gidanta ta umurcesa yaje ya hado musu breakfast, ya fita da sauri."

Zuwaira ta kalleta sama da kasa "Haba Husaina dubi shigarki fa sannan kika yaron gidanki har cikin bedroom dinki?"
"Look Zuwaira nu dake duk kanwar ja ce fa, jirgi daya ya kwaso mu, ya saba shigowa sai me?"
Ta gyada Kai "No duk rashin da'ata ba zan bar wani kato ya shigo min cikin dakin barcinmu ba don na dauke shi matsayin *sacred secret place*

"Hhhmmm ba dai kin koshi ba? Mu bar zancen mu koma na dalilin nemanki, shin ina Alhajin da yaso like miki wajen bukin nan, ya dameni in bashi lambar wayarki, ya isheni da naci that's why na kiraki tunda safe, me ye ra'ayinki?"

Tayi saurin girgiza Kai "Raba da wuya kinji, in don kayan da muka ce muna so ne zamu sara ya taimaka mana ya bar abinsa, irinsu sun cika mita kawai ya hana min sikit.. Ni dai yanzun Kinga fuskata ko? Wallahi aikin Baba da Mama ne suka taru sukai min sukuwar Sallah don nace ban amince Haseeb yai aure ba."

Ta furzar da ruwan da sanyin data kurba ta bugi kirji cikin tsoro "Dr Haseeb zai yi aure? Wonderful...
"Kin ganni nan fa cikin tashi hankali nike, that's na garzayo bidan shawarki don iyayena sun bashi go ahead."

"Yo inya sakeki ba kin huta ba, ga masu sonki ido rufe?"

Tace "Sakin bai dameni ba, hakan nike so Amma wallahi ba zan bar gidansa kafin aurensa ba wannan yarinyar ta dauka ta isa ta koreni, sai tazo ta zauna na nuna mata ruwa ba sa'an kwando bane, wutsiyar rakumi tayi nisa da kasa."

Husaina tace "A ina ya samu matar ne?"

Ta amsa "Matar kaninsa daya rasu dinnan nan, shine iyayenta suka cusa mata ita don sun ga da maiko."

"Tashin hankali inji Husaina ta Fadi cikin karaji "Yarinyar dake teaching makarantar kurame?"

"Yes ita, wani abu ne?"

Ta kada Kai "Yadda nike ji yarinyar nada kamun Kai da rike addininta, Kinga ko nan an samu difference.

"Wannan lalurar tace Husaina ta Fadi tana daga kafada irin bai dameta ba dinnan, fada min meye shawara yanzun?

Tayi shiru tukunna kafin tace " yanzun Kam kwantar bauna za muyi mu jira ta tare sai ki bullo da kissa da munafunci hade da karfar baka Wanda yafi asiri aiki mu gama da ita. Da dai baki da niyyar barin gidan ne da mun hadata da malam Mai gobe da nisa."

Zuwaira tayi hamma tace "Shikenan sai mun sake haduwa, bari in koma gida don yau harda su Khalifa su Mama sunce in kwashesu, na baro an kaisu makaranta ne."

Tayi tagumi "Oh in banda abin Dakta meye na hadaki da iyaye Kuma, ya barki kiji da jinyar kololon bakin cikin daya mulmula ya saka miki a kahon zucci don kishi cuta ce."

Ta mike tsaye" Ki barsa kawai zan bashi mamaki, ni kam na tafi."

"Zan iskoki har gida ba sai kinyi wahalar dawowa ba, yi jinyar tsamin jikinki."

Yau kwana biyu kenan da taji labarin Hjy Kaltume na fama da zazzabi,tayi niyyar ta share ko ta aika kawai a dubota, Umma da Maryam sunce bai dace ba, ciwo ya kore komi Kuma tafi gaban sharewa a wajenta, ita tasan hakan illa dalilan da suka taso suka haddasa nisantar junansu.

Ba domin batun aurensu da ya taso ba ai Hjy Kaltume uwarta ce mai bata nono tasha ta koshi.Tuni ta daina jin haushinta sai kunya data karu fiye da dauri, ta bi maganar iyaye ta shirya zuwa dubo Hajiyar

Karfe takwas daidai ta fito daga gidansu sanye da wata doguwar riga ta yadin Kampala shadda maroon colour, wace ta dora Mata after dress a samanta cream colour.

Tafiyar cikin rashin karsashi a natse take yi alamar dole ne yasa ta fito.

Iskar dake bugawa a hankali ta rinka kada abayar da lullubinta, tafe take tana jan adduoin neman kariyar Ubangiji daga sharrin mazan dake ta son yi mata magana
Yau saita ga gidan Hajiyar yai mata nisa, iya kauda kanta Saida wani Mai motar ya kyala ido ya ganta, ya Kuma bi bayanta har zuwa daidai lungun da zata shiga kwanar gidan Hajiyar, yai parking ya fito ya tsaya jiran fitowarta....

Ta shiga tareda sallama, Mairo ta amsa cikin murna "Marhabin maman Abdul sai yau, idonki kenan?"
Tayi dan dariya "Kinada bakin magana ke sau nawa kika taho wajena?".
"Ai kuwa sai dai ki zargeni na kanje in duba Umma mana" Mairo ta kare kanta...

"To ai shikenan ya jikin Hajiya?"
"Da sauki kin San halinta ai bata son a ga gazawarta."
Rahima tace "In shiga in ganta, Allah ya sauwake.

Hjy Kaltume na kwance bisa katuwar katifar da aka fito mata da ita falo, ta dago kai, tunda taga bakuwarta ta tashi ta zauna "Ni fa naji kamar muryarki sai naki amince ke dince tunda kin gujeni Rahima, Ina dan gidan Baba?"

Rahima ta zauna kusa da ita daf da katifar ta gaisheta tukunna kana ta ajiye ledar data riko mata lemu da ayaba tace "Allah ban gujeki ba Hajiya hidimomin ne sukayi yawa, Abdul na baro sa gida naga darene yasa bance ya rakoni ba, Su Baffa da Umma na gaidaki da jikin."

Tace "Nagode Allah yai albarka Ina amsawa, ita Umma takan lekoni, nima nakan aiki Mairo ta dubota.".

Rahima tayi shiru, zuwa can ta tambayeta "Hajiya ko irin rashin lafiyar nan ce da kika taba yi bayan an kawoni ba dadewa?"

Ta amsa "Ina tsammanin shine, domin yanayin jikin nawa kasala ce ke rufeni inji ko hannuna ban iya dagawa balle inyi motsi mai karfi, ga rashin samun isashshen barci, dare ya tsala kiga kowa na barci Ni kuwa lokacin nawa idanun zasu bushe in kasa barcin in rasa kuzarin tashi in gabatar da kiyamul lail yadda na saba, shi yafi damuna."

"To kin sanar da Yaya kuwa?"
Ta kada Kai "Hhmmm wannan Yayan naku hidimomi sunyi masa yawa, baida kwanciyar hankali wallahi har tausayinsa nike ji shiyasa nayi biris da tawa lalurar."

"Hajiya ba'a yiwa ciwo haka fa, idan ya fahimci halinda kike ciki ba zaiji dadi ba, to Yaya Hayatu fa?"

"Shima bai sanin ba Yana can yana zirga-zirgan Shirin tafiyarsu Hajj."
Rahima tayi dan murmushi "Ai kuwa da sauran lokaci ko azumi ba muyi ba."
"To Rahima Mai kwarmin ido ba da wuri yake fara kuka ba? Duk da ba karamin kuzuri aka biya musu gara dai su nema su Kara saboda mutum bai San yanayin da zai kasance a kasar da ba tasa ba."
"Hakane gaskiya, zuwa Hajj Kam a wannan lokacin said mutum ya shirya, Allah yasa a dace.".

Hajiya tace "To ameen, tabarbarewan al'amurran kasarmu sai addua."

Rahima ta tuna dare ne ba rana ba, ta yunkura ta mike tace "Hajiya dare nayi bari in isa gida Zan dawo in an kwana biyu.'

Ta bita da kallo kawai na ciki na ciki, tana son yi mata maganar Daktan ta kasa, Rahima na jin nauyinta kar ta matsa Mata, taja baki ta tsuke... Kafin suyi sallama amon muryar da kesa gabanta faduwa ce ta tsinkayo yana magana da Mairo... Nan take kirjinta yai mata nauyi sanadiyyar bugawar da zuciyar keyi ba control, tun kafin ya iso kamshin turarensa ya Kara tabbatar mata da shigowarsa.

Ta mutu a tsaye, gaga tsara gaga, wannan shine gaba damisa baya siyaki, Ina zata shiga, uwardakin Hajiya ko saurin ficewa?
Ta juya kwakwalwarta tayi dim ta tsaya cak! taki aiki balle taba sauran sassan jikinta umurnin next step da zata dauka.

Ya kunno kai cikin dakin bayan Hajiya ta amsa sallamarsa, Yana shiga ya doshi gefen katifar uwar ya zauna, ya dago ya kalli Rahima dake tsaye a sandare yace "Ba dai har zaki tafi ba, daga can gida nike Umma tace kina nan."

Da za abata zabi da basu ko gaisa ba ta sulale ta gudu that's in tafiyar zata yuwwu mata kenan da gwiwoyin da suka yi sanyi har kafafunta na rawa, nan ta durkushe ta gaisheshi.

Amsar da ya bata cikin sakin fuska ya bata mamaki, eh to a gaban Hajiya ai ba zai rinka wannan cin maganin ba a nata tunanin.
Cike da farin ciki da jin dadi ta kallesu "Ko zaka rage mata hanya ne tunda tayi shirin tafiya?".

Rahima ta girgiza Kai "Hajiya tafiyar guda nawa ce, ba komi nagode yanzun zan Kai gida, mu kwana lafiya, Allah ya Kara sauki."

Dr Haseeb yayi dan murmushinsa ba tare da yace komi ba.
Hajiya tace "To shikenan Allah ya bamu alkhairi, nagode Allah sa albarka."

Da hanzarinta ta fito waje ta saki wata ajiyar zuciya amma me zata gani? Mutumin dake jiranta ya fito daga mota ya karaso wajenta "Salamu Alaikum don Allah Hajiya ina son magana dake."

Ta kalleshi a tsorace ta amsa "Nima don Allah kayi hakuri bani da lokacin magana da Kai."

Babban mutum ne da ganinsa bata son cin mutuncinsa amma bai fahimci hakan ba ya sake matsawa kusa "Yi hakuri ki bani minti biyar kacal, sunanki da uguwarku nike son sani tunda kina sauri yanzun ki bani time in taho gida ga compliment card dina."

"Hajiyar ta gode rike card dinka don bata bukatar sanin sunanka an riga anyi mata miji.". Bata yi aune taji muryar Haseeb na maida jawabi.

Mutumin ya kalli Rahima yaji bata musa ba, ya kalli Haseeb duk da yana sanye da bakin glass dinsa fuskar nan ba alamun rahama nan da Nan yace "Don Allah kuyi hakuri sai anjima. Suna kallonsa ya shiga mota ya tafi.

Sun dade ba tareda cewa juna kanzil ba, ta tuna gida zata tafi, ta juya tace 'Nagode, ta fara tafiya...
Ya bita da kallo "Na yiwa Hajiya alkawarin kai ki so ki shiga mota mu tafi or are you ready for that kind of attention irin Wanda ya faru yanzun?"

Cikin siriryar murya tace "Ni bani na kirashi ba..

"Ba zarginki nayi ba, mu tafi ko?"

Tare suka shiga motar yaja suka isa cikin minti goma kacal. Motar na tsayawa ta bude kofar ta fito tace "Nagode a gaida su Aunty"

Ya waigo "Magana nike dauke da ita ko kina jin barci gobe na dawo?"

Ta girgiza Kai "Ba damuwa, mu shiga daga soro ko?"

Ya fito ta rufe motar yana biye da ita, suna shiga tace "Zan amso key din dakin baki.

Ta wuce cikin gida ta shaidawa Umman tana tareda bakone, Umman cikin farin ciki take wanda bai misaltuwa don ta gane waye ta Rahima ta kira bako. Har zata fita tace "Haka ake tarbon bakon ko ruwa ba zaki Kai masa ba balle lemu? Ban sanki da rowa ba Rahima."
Ba tareda da tanka ba ta bude fridge ta dauko gorar ruwa da lemo da cup ta dora bisa faranti ta koma soron, Yana ganinta ya mika hannu ya amshi kayan ta bude kofar tace "Bismillah."

Bayan sun shiga ciki ya ajiye farantin ya zauna kan kujera, Saida ta durkusa ta zuba lemun a cup ta ajiye sannan ta zauna gefen tabarma.
Ya dan kurbi lemun kadan ya mayar ya ajiye yana kallonta ta cikin dark glasses dinsa yace "Ina Abdul dina ne ko har yayi barci?".
Ta daga Kai "Ya riga yayi barci."

Yace "Yaron dana san yana kai wajen sha daya bai kwanta ba sai anyi ta fama dashi?"

Tace "Ban da yanzun kuwa ko don bai jin dadi ne oho."
Ya bude baki cikin mamaki "Ya akayi ban sani ba, baki aiko min ba ko Hajiya?"
Can kasa tace "Don naga ba it's not that serious."..
"Ya akayi kika San hakan?" Yai tambayar a fusace.

Ta sunkuyar da Kai "An kai shi asibiti sunce malaria ne sun bada treatment shi yasa naga ba sai na aiko ba."
Ya gyara zama "Daga yau karki sake min haka, duk abinda ya shafesa wajibi a sanar dani komin kankantarsa do you get me?"
Ta daga kai alamar amsa.
Ya kalleta sai Kuma ta bashi tausayi, ya sassauta murya yace "Look why not a daura auren nan this week mu ragewa kanmu jidali tunda Allah ya kaddaro mana haka, daman shawarar dana zo mu hadu mu yanke kenan. Mu ba yara bane, mun San ciwon kanmu naga zaifi dacewa ayi abinda iyaye keso zai fi mana sauki...

Rahima tayi shiru yaci gaba "Ko Hajiya abinda ke damunta kenan saboda ta sanya abin a ranta."

Ta dai kyalesa ya shirya mai yuwwa tana saurarensa yayi ya gama, ya mike zai tafi ya mika mata rafar kudi tareda tsadaddar handset.

Cikin kwanaki uku kacal aka gama tsarawa da shirya komi. Daktan ya aika kayan aurensa akwatuna biyar, ya shaida mata ba zai ajiyesu gida daya da Zuwaira ba ya nemi amincewar yazo su tafi taga gidan da ya saya

Showing 39001 words to 42000 words out of 79962 words

  • 12
  • 13
  • 14
  • 15
Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14 Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27
Chapter 14 Reading Rahima Complete Hausa Novel.txt (2025)

References

Top Articles
Latest Posts
Recommended Articles
Article information

Author: Zonia Mosciski DO

Last Updated:

Views: 5496

Rating: 4 / 5 (71 voted)

Reviews: 94% of readers found this page helpful

Author information

Name: Zonia Mosciski DO

Birthday: 1996-05-16

Address: Suite 228 919 Deana Ford, Lake Meridithberg, NE 60017-4257

Phone: +2613987384138

Job: Chief Retail Officer

Hobby: Tai chi, Dowsing, Poi, Letterboxing, Watching movies, Video gaming, Singing

Introduction: My name is Zonia Mosciski DO, I am a enchanting, joyous, lovely, successful, hilarious, tender, outstanding person who loves writing and wants to share my knowledge and understanding with you.